Wayar hannu manhaja ce ta Hausa da aka ƙirƙira domin samar da wuri na musamman ga matasa da sauran masu amfani da harshen Hausa domin nishaɗi, ilmantarwa, musayar ra'ayi da sadarwa.
A cikin manhajar za ka iya samun abubuwa daban-daban kamar Gidan Kallo, Abokai, Gida, Fira, Rayuwata da Koyon AI. Manufar manhajar ita ce haɗa masu amfani wuri guda domin su samu damar koyon abubuwa masu amfani, yin sabbin abokai, tattaunawa da juna da kuma raba abubuwan da suke da amfani.
Fira: Za ta ba masu amfani damar tattaunawa da juna cikin sauƙi, kamar yadda ake yi a kafafen sada zumunta. Mai amfani zai iya nemo wasu masu amfani sannan ya fara hira da su.
Abokai: Wuri ne da masu amfani za su iya gano sauran masu amfani da manhajar tare da ƙulla sabuwar alaka ta abota.
Rayuwata: Wuri ne da mai amfani zai iya bayyana abubuwan da yake son rabawa da sauran mutane.
Koyon AI: Sashe ne da aka tanada domin taimaka wa masu amfani su fahimci fasahar Artificial Intelligence (AI) da yadda za su yi amfani da ita wajen karatu, aiki, kasuwanci da ƙirƙirar abubuwa masu amfani.
Muna fatan Wayar hannu za ta zama ɗaya daga cikin manhajojin Hausa da za su taimaka wajen haɗa mutane, ƙarfafa ilimi, ƙirƙira da ci gaban matasa.
More education apps in Hausa.